NATIONAL DIWANI MAIDUGURI 2023
JAN HANKALI GAME DA SALLAR ASUBAH .... KARANTA ✍️ • Sallar Asubah itace Mafi Alkhairi Fiye da Bacci , Mu rage Bacci Don Mu ribanta da Goben mu, • Bacci Amsawar Zuciya ne Ita Kuwa Sallah Amsawar kiran Ubangiji ne • Shi Bacci mutuwa ne Ita Kuwa Sallah Rayuwa ce • Shi Bacci Hutu ne na gangar Jiki Sallah Kuwa hutu ne na Ruhi • Bacci da Mumini da kafiri Duk Suna Yinsa Ita Kuwa Sallah Musulman kwarai sune Kadai ke yinta. Masu tashi lokacin ketowar Alfijiri sun Rabauta , Fuskarsu kuma ta Haskaka Goshinsu kuma Yayi Haske da Kyalli , Lokacinsu kuma yayi Albarka, idan Kana cikinsu toh Ka godewa ALLAH da Ya Fifita ka, Idan Kuwa baka cikinsu toh Ka Roki ALLAH Ya saka Cikin su, MENENE YAFI ALFIJIR KYAU ? • Farillarsa {Sallar Asuba} zata Saka ka Acikin Kulawar Ubangiji • Sunnarsa (Rak'ataanil fajr) tafi Duniya da Abinda Ke Cikinta {Hadeeth} •️ Ita Sallar Asubah da Mala'iku masu aikin dare da Mala'ik...