Skip to main content

JAN HANKALI GAME DA SALLAR ASUBAH .... KARANTA ✍️


 JAN HANKALI GAME DA SALLAR ASUBAH   .... KARANTA ✍️ 


• Sallar Asubah itace Mafi Alkhairi Fiye da Bacci , Mu rage Bacci Don Mu ribanta da Goben mu, 


• Bacci Amsawar Zuciya  ne Ita Kuwa Sallah Amsawar kiran Ubangiji ne 


• Shi Bacci mutuwa ne Ita Kuwa Sallah Rayuwa ce 


• Shi Bacci Hutu ne na gangar Jiki Sallah Kuwa hutu ne na Ruhi 


• Bacci  da Mumini da kafiri Duk Suna Yinsa Ita Kuwa Sallah  Musulman kwarai sune Kadai ke yinta.


Masu tashi lokacin ketowar Alfijiri  sun Rabauta , Fuskarsu kuma ta Haskaka Goshinsu kuma Yayi Haske da Kyalli , Lokacinsu kuma yayi Albarka, idan Kana cikinsu toh Ka godewa ALLAH da Ya Fifita ka, Idan Kuwa baka cikinsu toh Ka Roki ALLAH Ya saka Cikin su, 


MENENE YAFI ALFIJIR  KYAU ?

• Farillarsa {Sallar Asuba} zata Saka ka Acikin Kulawar Ubangiji 


• Sunnarsa (Rak'ataanil fajr) tafi Duniya  da Abinda Ke Cikinta {Hadeeth} 


•️ Ita Sallar Asubah da Mala'iku masu aikin dare da Mala'iku masu aikin safe duka suna Halartar ta, 

Ya kai Dan'uwa, Ya ke Yar'uwa musani Duk Wanda Ya rayu Akan wani aiki toh akansa zai Mutu, Wanda Ya Mutu kan wani Aiki kuma Akansa za'a tashe shi.


Idan ka Karanta wannan sako kuma kayi aiki Dashi zaka samu Ladan Aikin ka, idan kuwa katura (shre)zaka samu Kwatankwacin ladan wanda ya aikata (Hadith)


Kada ka 6oye ilimi, ka Bayyana shi, Zaka Samu Kyakkawan Sakamako, 

Kuyi murna ya ku Masu Sallar Asubahi

Comments

Popular posts from this blog

NATIONAL DIWANI

 NATIONAL DIWANI 

NATIONAL DIWANI MAIDUGURI 2023

  NATIONAL DIWANI MAIDUGURI 2023

SUNAYAN "YA"YAN SHEHU IBRAHEEM INYASS R.T.A GUDA (75)

SUNAYAN "YA"YAN SHEHU IBRAHEEM INYASS R.T.A GUDA (75)                  DAGA    ZAWIYYA KUSFA  1.shehu abdullahi inyass  2.shehu ahmad dam inyass  3.shehu ahmad tijjani inyass  4.shehu muhammadul mahi inyass  5.shehu muhammadul amin inyass  6.shehu muhammadu muj'taba inyass  7.shehu muhammadu nazir inyass  8.shehu muhammadu hadi inyass  9.ehehu muhammadul makiyu inyass  10.shehu muhammadul mamunu inyass  11.shehu muhammadul akibu inyass  12.shehu muhammadul muntaka inyass  13.shehu muhammadul arabi inyass  14.shehu muhammadul mukhtar inyass  15.shehu muhammadu nasir inyass  16.shehu muhammadul mahdi inyass  17.shehu muhammadu murtadha inyass  18.shehu muhammadu shafi'u inyass  19.shehu muhammadan takiyan khairul bariyati inyass  20.shehu muhammadul ahad inyass  21.shehu muhammadu abdurrahim inyass  22.shehu muhammadu kuraish ...