BAYANIN SHEHU RTA AKAN SALATIL FATIHI (1)
Shehu rta yake cewa: ita Salatil fatihi Al'amari ne na ubangiji wanda hankali baya shigansa, sai dai cewa ita ta sauka ne ta hanyar ilhama, sau dayawa kuwa ma'anar wahayi takan zama ilhama.
1. Akwai wahayin da Allah yakeyi a cikin hakkin Annabawa
وَمَا كَانَ لِبَشَرٍ أَنْ يُكَلِّمَهُ اللَّهُ إِلَّا وَحْيًا (الشورى 51)
Ma'ana: Ɗan Adam bai kasance wanda Allah zaiyi magana dashi ba saidai ta hanyar wahayi.
2. A cikin Hakkin Waliyai, Allah yana cewa:
وَإِذْ أَوْحَيْتُ إِلَى الْحَوَارِيِّينَ (المائدة 111)
Ma'ana "A yayinda nayima Hawariyawa wahyi
3. A cikin hakkin Ɗan Adam Allah yana cewa:
وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ أُمِّ مُوسَىٰ أَنْ أَرْضِعِيهِ (القصص 7)
Ma'ana :Munyi wahyi zuwa ga Mahaifiyar Musa (Annabi) da ta shayar dashi.
4. A hakkin sauran dabbobi Allah yana cewa:
وَأَوْحَىٰ رَبُّكَ إِلَى النَّحْلِ (النحل 68)
Ma'ana: ubangijinka yayi wahayi izuwa ga Kudan zuma.
Muradi da wahayi anan shine Ilhama, shiriya da Shiryarwa, kowani ɗaya daga cikin wadannan yanada ma'ana kebantacce.
A cikin jawahirul ma'ani shafi na 241 zakasamu bayani da da rarrabe- rarraben wahyi wanda zai shayar da kishirwarka.
Haƙika Maulanmu, sanadinmu, Masoyinmu shehu tijjani rta yayi mgna akan salatil fatihi yayinda aka tambayeshi. Shehu tijjani rta yace Annabi S.A.W yabashi labarin cewa: Salatil fatihi ba Ta'alifin Bakari bane, saidai cewa shi ya fuskanci Allah da ibadu stawon lokaci kan Allah yabashi Salatin da ta nannaɗe dukkan lada da sirrin salatai a cikin ta
Ya daɗe yana neman haka sai Allah ya Amsa masa mala'ika yazomasa da rubutun salatil fatihi a takardan Haske.
Shehu tijjani rta yace: yayin danayi ta'ammuli da wanan salati sai nasameta ibadar Aljanu da mutane da Mala'iku bazasu aunata ba, har zuwa inda Shehu tijjani rta yake bada Amsar tambar da akayima cewa:
wai Salatil fatihi ta fita daga musuluci kuma annabi SAW bai wajabta ta ba.
Yabada amasa dacewa: Ita kaifiyyar salatil fatihi waridi ne daga Gaibu kafin ita kuma bai taɓa tabbata akwai wani salati waridi daga gaibu ba.
Salatil fatihi ta fita daga dukkan ƙa'idodin da aka sani, ba ta'alifin mawallafi bane tafi gaban Haka, amma akwai kaifiyyar salati wanda aka samu daga Annabi s a w wanda ake ibada da ita.
Kadda ku kalli maganganun faƙihai akan salatil fatihi har zuwa inda yake cewa: kar ku kalli maganganun makaryata masu karyata salatil fatihi ko sukan mai sukan salatil fatihi, falala a hanun Allah take kuma yana bawa wanda yaso. Falalar Allah kuwa ta fita daga da'iran ƙiyasi. Ya iksheka faɗin Allah ta'ala
ويخلق ما لا تعلمون (النحل 8)
Ma'ana: Zan halicci abinda baku sani ba.
Wannan shine abinda lokaci yabamu damar rubutawa, zuwa wani lokacin Allah zaiyi Abinda yaso insha Allah
Allah yasanyamu daku gaba ɗaya cikin mu'utaƙidai (masu imani ) yakuma azurtamu da fahimta dan baiwarsa ka karamcin sa.
Wassalam
Ibrahim niyass

Shukran
ReplyDelete08026895611
ReplyDelete08026895611
ReplyDelete08026895611
ReplyDelete