Skip to main content

BAYANIN SHEHU RTA AKAN SALATIL FATIHI (1)


 BAYANIN SHEHU RTA AKAN SALATIL FATIHI (1)


Shehu rta yake cewa: ita Salatil fatihi Al'amari ne na ubangiji wanda hankali baya shigansa, sai dai cewa ita ta sauka ne ta hanyar ilhama, sau dayawa kuwa ma'anar wahayi takan zama ilhama. 


1. Akwai wahayin da Allah yakeyi a cikin hakkin Annabawa


وَمَا كَانَ لِبَشَرٍ أَنْ يُكَلِّمَهُ اللَّهُ إِلَّا وَحْيًا (الشورى 51)


Ma'ana: Ɗan Adam bai kasance wanda Allah zaiyi magana dashi ba saidai ta hanyar wahayi.


2. A cikin Hakkin Waliyai, Allah yana cewa: 


 وَإِذْ أَوْحَيْتُ إِلَى الْحَوَارِيِّينَ (المائدة 111)


Ma'ana "A yayinda nayima  Hawariyawa wahyi


3. A cikin hakkin Ɗan Adam Allah yana cewa: 


وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ أُمِّ مُوسَىٰ أَنْ أَرْضِعِيهِ (القصص 7)


Ma'ana :Munyi wahyi zuwa ga Mahaifiyar Musa (Annabi) da ta shayar dashi.


4. A hakkin sauran dabbobi Allah yana cewa:


وَأَوْحَىٰ رَبُّكَ إِلَى النَّحْلِ (النحل 68)


Ma'ana: ubangijinka yayi wahayi izuwa ga Kudan zuma.


Muradi da wahayi anan shine Ilhama, shiriya da Shiryarwa, kowani ɗaya daga cikin wadannan yanada ma'ana kebantacce. 


A cikin jawahirul ma'ani shafi na 241 zakasamu bayani da da rarrabe- rarraben wahyi wanda zai shayar da kishirwarka.

Haƙika Maulanmu, sanadinmu, Masoyinmu shehu tijjani rta yayi mgna akan salatil fatihi yayinda aka tambayeshi. Shehu tijjani rta yace Annabi S.A.W yabashi labarin cewa: Salatil fatihi ba Ta'alifin Bakari bane, saidai cewa shi ya fuskanci Allah da ibadu stawon lokaci kan Allah yabashi  Salatin da ta nannaɗe dukkan lada da sirrin salatai a cikin ta  


Ya daɗe yana neman haka sai Allah ya Amsa masa mala'ika yazomasa da rubutun salatil fatihi a takardan Haske. 


Shehu tijjani rta yace: yayin danayi ta'ammuli da wanan salati sai nasameta ibadar Aljanu da mutane da Mala'iku bazasu aunata ba, har zuwa inda Shehu tijjani rta yake bada Amsar tambar da akayima cewa: 


wai Salatil fatihi ta fita daga musuluci kuma annabi SAW bai wajabta ta ba.


Yabada amasa dacewa: Ita kaifiyyar salatil fatihi waridi ne daga Gaibu kafin ita kuma bai taɓa tabbata akwai wani salati waridi daga gaibu ba.  


Salatil fatihi ta fita daga dukkan ƙa'idodin da aka sani, ba ta'alifin mawallafi bane tafi gaban Haka, amma  akwai kaifiyyar salati wanda aka samu daga Annabi s a w wanda ake ibada da ita. 


Kadda ku kalli maganganun faƙihai akan salatil fatihi har zuwa inda yake cewa: kar ku kalli maganganun makaryata masu karyata salatil fatihi ko sukan mai sukan salatil fatihi, falala a hanun Allah take kuma yana bawa wanda yaso. Falalar Allah kuwa ta fita daga da'iran ƙiyasi. Ya iksheka faɗin Allah ta'ala 


ويخلق ما لا تعلمون (النحل 8)


Ma'ana: Zan halicci abinda baku sani ba.


Wannan shine abinda lokaci yabamu damar rubutawa, zuwa wani lokacin Allah zaiyi Abinda yaso insha Allah 

Allah yasanyamu daku gaba ɗaya cikin mu'utaƙidai (masu imani ) yakuma azurtamu da fahimta dan baiwarsa ka karamcin sa.


Wassalam 

Ibrahim niyass

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

NATIONAL DIWANI

 NATIONAL DIWANI 

NATIONAL DIWANI MAIDUGURI 2023

  NATIONAL DIWANI MAIDUGURI 2023

SUNAYAN "YA"YAN SHEHU IBRAHEEM INYASS R.T.A GUDA (75)

SUNAYAN "YA"YAN SHEHU IBRAHEEM INYASS R.T.A GUDA (75)                  DAGA    ZAWIYYA KUSFA  1.shehu abdullahi inyass  2.shehu ahmad dam inyass  3.shehu ahmad tijjani inyass  4.shehu muhammadul mahi inyass  5.shehu muhammadul amin inyass  6.shehu muhammadu muj'taba inyass  7.shehu muhammadu nazir inyass  8.shehu muhammadu hadi inyass  9.ehehu muhammadul makiyu inyass  10.shehu muhammadul mamunu inyass  11.shehu muhammadul akibu inyass  12.shehu muhammadul muntaka inyass  13.shehu muhammadul arabi inyass  14.shehu muhammadul mukhtar inyass  15.shehu muhammadu nasir inyass  16.shehu muhammadul mahdi inyass  17.shehu muhammadu murtadha inyass  18.shehu muhammadu shafi'u inyass  19.shehu muhammadan takiyan khairul bariyati inyass  20.shehu muhammadul ahad inyass  21.shehu muhammadu abdurrahim inyass  22.shehu muhammadu kuraish ...